🎵

Iye

Album: Iye Durasi: 3:08

Iye!

Na namu, na namu

Toh munfito ku fito mu soma

Abun ga na lokachi wataran baza mu yaba

Iye!

Sama kai! Haba (Iye!)

Sultan with the beat baby

Ahh ahh, ki dauki zare ki bar auduga, kinji? Kinji

Dawa ke da tsangarniya yar uwata

Ki dauki zare ki bar auduga, in kinji? Kinji ni

Dawa ke da tsangarniya (Ah haiye!)

Ah haiye ke kaza da tonai, tonai

Bana kar ki tono an yanka ki dan kaddara

Tafi fata

(Sama, kasa, sama)

Kaddara tafi fata

(Haka, haka) Ah haiye kaddara tafi fata

A gwara ku daina ma raia lu'ou-lu'ou dan ganin bai da nauyi In wuta ta dake shi abun ado ne

Iye!

Ah yai! Ga muryar mu ta kewaya

Kafin yanzu mun sha wuya

Mata sun ji kidan mu ya faifaya

(Ha-ha-ha-ah haiye)

Rawa hardda jinjinniya

Kwado ke da tsallen tsiya

Mu kidan namu ne amman salon yan gari

Kunji mata?

Lallai da masu gari ake cin gari in babu dan gari bako ma ga mai zaya chi, hayai!

Iye!

Sama kai, sama

Iye!

Ah yai ruwa ya kore shuka

Ma kwar ruwa sai a tashi

Bana dai babu harka (Iye!)

Kai maciji yaga shaho ya antaya kai a rami

Ya bar baya a titi (Iye! Ashe zaka charhi)

Har yanzu Baba yana nasihar sa Inna tana nasihar ta

Amman Aunty kwalba kau ai anki a daina sharri (Iye!)

Kai ta yaya zata daina? Na Gwanja dauki sauti

Rawa ta kama gurgu zama ba namu ne ba

Ah yai mai kazafi Allah yana kallon ka

Kai ta tayi dangi suna zundan ka

Allah bamu ido ranar ganin karshen ka mugu

Kai girbi wa shukar ka

Kai tata chi ta cutar ka

Ai ta gani a kwaryar ka

Ai dolle ma ya gani a kwaryar sa barshi kawai da halinsa

Kowa akwai abincin sa ba sai yayi hassada ba idan lokachi ya ishe mana zamu daina, (Iye!)

Ah yai gwara ku daina haushi da mu

Allah ne yakeyi damu

Ko kun kama suna da mu

(Kuma) Ai ko kuki kama suna da mu

Mu mun samu dai dai da mu

Ko kuna kin mu tofa dubu suna yi damu munji gata

Toh ai su Barmana Choge ma sun tafi Allah bamu sa'ar zuwa su yan adawar mu dukka a bar su gadin gari

Iye!

Oh my God

It's Sultan on the beat